<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Me Za Mu Ce da Yesu? Ɗan Ragon Allah Ne LW106</title>
<lyrics>[V1]
 1) Me za mu ce da Yesu? Ɗan Ragon Allah ne.
 Mai ɗauke kayan zunubi na duk jama'a ne.
 Ka ba ni wannan sani, azabar da ka sha.
 Mai Gaskiya, Mai Tsarki, ka ɗauke laifina

[V2]
 2) A cikin sa'ar mutuwa Mai Cetonmu ya ce,
 &quot;Uba, yi musu gafara, sun yi a jahilce.&quot;
 Ka ba ni wannan sani, alherin da ya sa
 Maɗaukaki, Mai Tsarki, ya ɗauke laifina.

[V3]
 3) Rana ta rufu sarai, duniya ta duhunta,
 A Sama duk mala'iku sun kasa dubawa.
 Ka koya mana sanin wannan asirinka,
 Dalilin da Mai Tsarki ya ɗauke laifina.

[V4]
 4) Azaba duk ta wuce, Mai Nasara ya ci.
 A hannun daman Allah ne ya tsaya, Maɗaukaki.
 Ka koya mana sanin iko na tashinka,
 Mai Tsarki, Mai Nasara, Yesu Mai Cetona.</lyrics>
<hymn_number>106</hymn_number>
</song>